NLO TA BA DA DALILI NA SAUYA A  LOKACIN FARA GASAR 2023

0
173
NLO TA BA DA DALILI NA SAUYA A  LOKACIN FARA GASAR 2023
DAGA  MUSBAHU BALA YAN GURASA
Gasar da ake ta jira  a fara ta, ta 2023 ta Gasar Wasannin mai daraja ta uku ta Kasa (NLO),wacce kalandar ta za ta fara aiki a hukumance ranar Laraba 3 ga Mayu, bisa ga umarnin Sakatariyar hukumar.
 Duk da cewa an dage gasar har sau biyu a lokacin da ake shirin fara buga wasannin, kamar yadda ta yi alkawari ga kungiyoyin. Izuwa yanzu dai Sakatariyar gasar ta kimtsa tsaf kuma komai na  ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara
 Jadawalin kakar  wasannin da  yana kan turba a halin yanzu bayan an amince da shi a taron hukumar,wanda  aka yi bayan dagewar ta baya,sannan  aka amince da shi a watan Fabrairu da daga taron masu ruwa da tsaki NLO  bisa yin la’akari da kalubalen tsaro, tattalin arziki da siyasa a kasarnan.
 A cewar sashin yada labarai na NLO, wata sanarwa a hukumance da ta fitar  a ranar Alhamis ta ba da dalilai na sauyin.
 “I ziuwa yanzu komai  kan turba don fara kakar wasa ba tare da an samu  da ansamu tsaiko ba, dangane da kayan aiki  da dukkanin abubuwan da ake da bukata, har zuwa filayen  wasannin
in ji Babban Jami’in Gudanarwa na NLO (COO) Olushola Ogunnowo.
 “A daya bangaren kuma, wasu kungiyoyi sunyi sanya saboda har yanzu ba su kammala rajistar ‘yan wasan su ba.
 “Yin rijistar ‘yan wasa da duk kungiyoyin ke yi kafin a fara kakar wasa ta bana, yana da matukar muhimmanci ga NLO, domin ba al’adarmu ba ce mu fara kakar wasa da tsarin na a gaggauce
 “Mun kuma yi la’akari da gasar,Federation Cup wanda yake a zagaye na 32.  Kuma  wasu daga cikin Ƙungiyoyin NLO har yanzu suna cikin  kofin, don haka ba zai zama adalci ba idan Sakatariyar ba ta yi la’akari da irin waɗannan ƙungiyoyi ba lokacin da aka fitar da tsarin  wasanni na wannan kakar wasa ba.
 Ogunnowo ya jaddada “Bayanin cewa hakan yasa aka kara mako guda  da ranar farawa, muna da tabbacin cewa kungiyoyin da abin ya shafa za su yi amfani da wannan taga don kammala rajistar ‘yan wasan su a kakar wasa ta bana.”
 A halin da ake ciki, kungiyar ta NLO za ta karbi bakuncin taron manema labarai a Legas ranar Laraba 26 ga Afrilu, inda za ta fidda wata gagarumar sanarwa dangane da sabbin masu daukar nauyinta. da dabaru da muka sanya don Tsarin Gasar Wasanni,” in ji Babban Jami’in Gudanarwa na NLO (COO) Olushola Ogunnowo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here